Isa ga babban shafi

Atiku ya gindaya sharadin ajiye takaddamarsa da Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya  kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a shekarar 2023, Atiku Abubakar ya gindaya sharadin ajiye takaddamarsa da shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa kotu ce za ta raba su.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar © premium times
Talla

Atiku wanda ya zo na biyu a zaben da aka gudanar a farko-farkon shekarar 2023 ya kalubalanci nasarar da Tinubu ya samu a Kotun Sauraren Kararrakin Zabe, amma kotun ta tabbatar da nasarar shugaban na Najeriya.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren karin bayanin da Atiku ya yi wa manema labarai a Abuja.

Sai dai duk da hukuncin na kotun, Atiku ya karkata hankalinsa zuwa ga wata kotun Amurka wadda daga bisani ta bai wa Jami'ar Chicago umarnin fallasa takardun karatun Tinubu, takardun da Atikun ya ce, zai yi amfani da su wajen daukaka kara a Kotun Kolin Najeriya.

Atiku ya ce, akwai banbance-banbance a tsakanin takardun da Tinubu ya gabatar wa INEC da kuma wadanda Jami'ar Chicago ta fitar, abin da ka iya mayar da Tinubu a matsayin haramtaccen dan takara a zaben na 2023 da tuni ya samu nasara.

Atiku da Tinubu
Atiku da Tinubu © Guardians

A yayin gabatar da jawabinsa a wannan Alhamis ga taron manema labarai a birnin Abuja, Atiku ya bayyana cewa, babu abin da zai sanya shi ya ja da baya a fafutukarsa ta kalubalantar Tinubu.

 

Tuni na daukaka kara a Kotun Koli kan Tinubu. Har sai kotun ta tabbatar da nasararsa, sannan zan janye wannan takardamar. Inji Atiku.

Atiku ya bayyana cewa, babu wata kotu sama da Kotun Kolin, saboda haka zai amince da duk hukuncin da ta yanke.

Koda aka tambaye shi kan ko yana fuskantar matsin lamba daga shugaba Tinubu, sai ya bayyana cewa, lallai shugaban na Najeriya ya nemi tura masa wata tawagar gwamnoni, amma bai ba ta damar ganawa da shi ba a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.