Isa ga babban shafi

Bankin Duniya da na Afirka za su bai wa Najeriya rance kafin karshen 2023

Gwamnatin Najeriya ta bayyana samun nasara a kokarin da take na karbar bashin dala biliyan 1 da rabi daga Bankin Duniya da kuma dala miliyan 80 daga Bankin Raya kasashen Afirka AFDB.

Dalar Amurka
Dalar Amurka REUTERS - Yuriko Nakao
Talla

Mahukuntan kasar sun ce, za a yi amfani da kudaden ne wajen aiwatar da ayyuka da dama da suka shafi muhimman fannonin tattalin arzikin Najeriya.

Yayin ganawa da manema labarai a Abuja, ministan kudin Najeriya Wale Edun, sun sa ran baki dayan dalar biliyan 1 da rabi na Bankin Duniyar ya shiga hannunsu kafin karshen shekarar bana, da zarar sun kammala cika sharuddan da Bankin ya gindaya musu.

Ministan ya kara da cewar sun samu rancen kudaden ne daga sashin Bankin Duniyar da ke bayar da bashin kudade marasa kudin ruwa domin tallafa wa ci gaban kasashe.

A makon da ya  gabata ne dai rahotanni suka ce gwamnatin Najeriya ta nemi karin rancen dala miliyan 400 daga bankin duniya, domin sanya wa cikin shirinta na tallafa wa iyalai miliyan 15 a fadin kasar, matakin da ta ce yana daga cikin jerin wadanda take dauka don ragewa marasa karfi radadin cire tallafin man fetur da ta yi.

A wannan wat ana Oktoba shugaban Najeriya Bola Tinubu yayi alkawarin fara biyan Naira 25,000 ga ‘yan Najeriya ko iyalai miliyan 15, wadanda za su shafe tswon watanni uku suna karbar tallafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.