Isa ga babban shafi

'Yan Najeriya sun koka bisa shirin ciyo bashin sama da dala biliyan guda

Da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun nuna rashin amincewarsu da bukatar mahukunta kasar na neman  sake ciyo bashin kudi  har Dalar Amurka biliyan daya da Rabi daga Bankin Duniya.

Birnin Legas a tarayyar Najeriya
Birnin Legas a tarayyar Najeriya AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

A cewar gwamnatin kasar, za a amfani da kudaden ko kuma bashin ne wajen aiwatar da ayyukan raya kasa dake cikin kasafin kudin kasar na bana.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Muhammad Kabir yusuf. 

A farkon shekarar 2023 ne, asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya yi gargadin cewa shekarar za ta kasance mai tsaurin gaske ga  tattalin arzikin duniya, sakamakon kalubalen da  Amurka, kungiyar Tarayyar Turai da kuma China ke fuskanta, na  raunin da karfin tattalin arzikinsu ke yi.

Shugabar asusun na IMF Christalina Georgieva ta ce sabuwar shekarar da aka shiga za ta kasance mafi tsauri kan 2022 da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.