Najeriya na shirin ciyo bashin naira tiriliyan 26
Gwamnatin Tarayyar Najeriya na shirin ciyo sabon bashin naira tiriliyan 26, inda aka yi hasashen cewa, jumullar bashin da za a bi kasar ya kai naira tiriliyan 100 da 18 a cikin shekaru 3 masu zuwa, kamar yadda wani bincike ya nuna.
Wallafawa ranar:
Binciken da jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriya ya nuna cewa an samu wannan adadi ne sakamakon nazari da aka yi a kan bashin da ake bin kasar a halin yanzu da kuma wanda take hasashen ciyowa daga shekarar 2024 zuwa 2026.
Kamar yadda sabon manufarta a kan kudi ya nuna, gwamnatin Najeriya na shirin karbar rancen naira tiriliyan 26 da biliyan 42 a tsakanin shekarar 2024 da 2026, kana ta nuna cewa za ta yi amfani da naira tiriliyan 29.92 a cikin shekaru 3 wajen biyan kudin ruwa na basukan da ake bin ta.
Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya za ta karbi rancen naira tiriliyan 7 da biliyan 81, a shekarar 2024, kasa da naira tiliyan 8 da biliyan 84 da ta yi hasashen karbowa a shekarar.
Bayanai a game da kudaden shiga da wandanda ake batarwa sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu naira tiriliyan 5 da biliyan 19 a watanni 7 na farkon wannan shekarar amma ta kashe tiriliyan 3 da biliyan 94 wajen biyan kudaden ruwa na basukan da ake binta.
Nazarin da jaridar ta Punch ta yi a game da wannan al’amari ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta fara daukar matakan mayar da hankali ga karbar rance daga cibiyoyin kudi na cikin gida a maimakon daga waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu