Isa ga babban shafi

Majalisar Najeriya ta bukaci a yi gwanjon barikokin 'yan sanda

Majalisar Dokokin Najeriya ta bukaci gwamnati ta yi gwanjon daukacin barikokin ‘yan sanda da ke fadin kasar a wani kokari na inganta rayuwar ‘yan sandan kasar.

Barikokin da 'yan sandan Najeriya ke ciki sun yi muni.
Barikokin da 'yan sandan Najeriya ke ciki sun yi muni. © AFP/Victoria Uwemedimo
Talla

Makalisar ta kafa hujja da cewa tsananin munin yanayin da barikokin ke ciki ya sa ba sa zama don haka ba su da wani amfani illa a yi gwanjon su.

Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum da masu hankoron kare hakkin fararen hula sun soki wannan yunkuri na gwanjantar da barikokin 'yan sandan.

Ku latsa alamaer sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da Rukayya Abba Kabara ta yi da Aminu Adam Gwale, wani dan gwagwarmayar kare hakkin fararen hula a jihar Kano da ke Najeriya.

Majalisar Dokokin ta Najeriya ta gabatar da kudirin ne bayan da Murphy Omoruyi  daga jihar Edo karkashin jam'iyyar LP ya fara gabatar da bukatar haka a ranar Alhamis.

Jami'an tsaron Najeriya yayin aikin sintiri a lokacin zabe.
Jami'an tsaron Najeriya yayin aikin sintiri a lokacin zabe. AP - Sunday Alamba

Mista Omoruyi ya kafa hujjar cewa, tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar kyautata aikin 'yan sanda ta 2020, kuma daya daga cikin manyan abubuwan da wannan doka ta kunsa shi ne, magance mummunan halin da 'yan sanda ke ciki a kasar.

A cewar dan majalisar, matsalar rashin kyawawan wuraren zama na 'yan sandan ta ta'azzara, inda har ta gagari kundila duk kuwa da matakan da aka dauka a can baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.