Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Ya kamata Najeriya ta fara tsarin mulki na shekara 6, babu tazarce

Dan takarar Shugaban Kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya bayar da shawarar fara amfani da wa'adin shekara shida a kujerar Shugaban Kasa kuma babu neman tazarce.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar © premium times
Talla

 

Hakan, a cewarsa, zai rage neman sake lashe zabe ko ta halin ƙaƙa ga masu rike da kujerar.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa da ya kira a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma bayar da shawarar a rika kammala dukkan shari'un zabe kafin a kai ga rantsar da wanda ya lashe shi.

Ya kuma ce hukuncin Kotun Koli kan nasarar Shugaba Bola Tinubu na makon da ya gabata, ya bar baya da kura matuka.

Atiku dai ya tsaya kai da fata cewa sam Tinubu bai ma cancanci ya tsaya takarar shugaban ba a zaɓen da ya gabata.

Dan takarar ya kuma zargi Kotun Kolin da kuma Hukumar Zabe ta Kasa da goyon bayan rashin gaskiya, damfara da kuma ɗaure wa ƙarya gindi.

A makon da ya gabata ne dai Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaben sannan ta yi watsi da ƙarar da Atiku da takwaransa na LP, Peter Obi suka shigar a gabanta suna kalubalantar nasarar.

Atiku dai ya yi wukar kugu da sakamakon binciken da ya ce ya yi a kan takardun karatun Tinubu a Jami'ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka, amma kotun ta ce ba ta da hurumin sake karbar sabuwar shaidar da ba a gabatar a kotunan kasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.