Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya za ta kashe Naira biliyan 7 wajen kwaskwarimar gidan Tinubu da Shetima

Gwamnatin Najeriya na shirin kashe naira Triliyan 7 akan gyaran gidajen Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shetima tare da wasu hidimdimu kuma masu kama da hakan. 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23 © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

‘Yan  Najeirya sun nuna rashin jin dadin su akan wani shirin fadar shugaban kasar wajen yiwa gidajen shugaban kasar Bola Ahemd Tinubu da na mataimakinsa Kashim Shetima, wanda zai lakume naira biliyan 7 tare da kuma batun sayo motocin aiki na  ofishin maid akin shugaban kasa sama da Naira biliyan 1.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, za a fitar da kudaden ne daga karin kasafin kudi N2.176trn da majalisar dokokin kasar ta zartar dake jiran karatu na biyu a ranar Talata.

Wannan dai na zuwa ne adaidai lokacin da kasar ke fuskantar wahalhalu sakamakon janye tallafin man fetur da hauhawar darajar kudaden waje wanda ya haifar da tashin farashin kayayyakin abinci.

‘yan  Najeriyar dai sun taba ta da jijiyar wuya aka wasu motocin alfarma da za’a sayo wa ‘Yan majalisar dokokin kasar 469 kan kudi naira miliyan 160.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.