Isa ga babban shafi

Tinubu ya nada wanda bai kware ba ya shugabanci babban bankin Najeriya - Babacir

Najeriya – Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya Babacir Lawal ya cacaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan nada mutumin da bai dace ba, wato Dr Yemi Cardoso ya shugabanci babban bankin kasar.

Ginin Babban Bankin Najeriya CBN da aka dauka a watan Nuwambar 2011.
Ginin Babban Bankin Najeriya CBN da aka dauka a watan Nuwambar 2011. AP - Sunday Alamba
Talla

Lawal yace baya ga rashin kwarewar da ake bukata wajen jagorancin babban bankin dake aiwatar da manufofin kudade na gwamnati, akwai shakku dangane da bayanan tarihinsa da ya gabatar saboda yadda aka musu sauye sauye.

Tsohon sakataren yace ofishin kwamishinan tsare tsare da Cardoso ya rike lokacin Tinubu na gwamnan jihar Lagos, bai kai mizanin da ake bukata na bashi kujerar gwamnan babban banki na kasa baki daya ba.

Lawal yace dan ya rike kwamishinan kudi na karamar jiha irin ta Lagos, daya daga cikin jihohi 36 dake Najeriya, bashi da kwarewar da ake bukata na rike mukamin jagorancin babban bankin kasa baki daya.

Sakataren yace gwamnatin na kuma bayyana cewar Cardoso ya shugabanci banki mai rassa 13 a Najeriya, sai dai bankin da ake magana rassan sa gaba daya a Lagos suke, banda guda 2 da aka yi a Warri da Benin.

Lawal wanda na kusa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne, sun raba gari lokacin da ya dauki Kashim Shettima Musulmi a matsayin mataimakinsa, abinda ya sa ya fice daga jam’iyyar APC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.