Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda 113 a cikin mako guda - Janar Buba

Najeriya – Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce dakarun ta sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 113 da kuma kama wasu sama da 300 da ran su, a ci gaba da samamen da suke kaiwa a yankuna daban daban da ake fama da matsalar tsaro a cikin mako guda da ya gabata.

Shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Taoheed Lagbaja
Shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Taoheed Lagbaja © Nigerian army
Talla

Daraktan dake kula da harkokin kafofin yada labarai, Manjo Janar Edward Buba yace bayan hallaka ‘yan ta’addan, sojojin sun kuma kama barayin ‘danyan man fetur 25 tare da ceto mutane 91 da aka yi garkuwa da su, baya ga kwato makamai 129 da albarusai 717.

Janar Buba yace yayin gudanar da sintiri, dakarun su sun kama masu kaiwa mayakan boko haram kayayyaki a Kukawa da Damboa da Manguno da kuma Konduga da ke jihar Barno, tare da hallaka mayakan su 17 da kuma kama wasu 16.

Daraktan yace an mika mutanen da aka kama da wadanda aka ceto ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakan da suka dace.

Sojojin Najeriya na gudanar da ayyukan samar da tsaro a sassa daban daban na kasar, ciki harda yaki da mayakan boko haram da barayin man fetur da kuma yaki da 'yan bindigar da suka addabi arewa maso yamma da kudu maso gabas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.