Isa ga babban shafi

Muna fuskantar manyan kalubalen shugabanci sosai - Shettima

Najeriya – Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bayyana cewar suna fuskantar kalubale sosai wajen tafiyar da kasar lura da dimbin matsalolin da suka addabeta a wannan lokaci dake bukatar magance su.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima © kashim shettima facebook
Talla

Yayin da yake karbar ministan Denmark, Dan Jorgensen da ya ziyarci fadar shugaban kasar dake Abuja, Shettima yace ya zama wajibi su lalubo hanyoyin tinkarar wadannan matsalolin dake yiwa ci gaban Najeriya tarnaki.

Shettima wanda ya bayyana shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai ilimi da kuma kwarewar da ake bukata wajen fitarwa Najeriya kitse a wuta, yace yana da kwarewar da ake bukata na jagorancim kasar domin samar mata da ci gaba.

Mataimakin shugaban yace duk da yake man fetur na sahun gaba wajen taka rawa nan da shekaru 10 masu zuwa, a matsayinsa na ginshikin tattalin arzikin Najeriya, sai dai a halin yanzu karsashinsa na iya dakushewa a shekaru masu zuwa, abinda ya sa ya zama wajibi su sake tunani domin lalubo wasu hanyoyin da kasar zata dogara da su.

Shettima yace wannan ya sa suka fara mayar da hankali wajen zuba jari a bangarorin fasaha da makamashin da baya gurbata muhalli da kuma wasu bangarori na daban.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana irin hasken da wannan bangare na fasaha yake da shi da kuma bangaren zuba jari ta hanyar makamashin da baya gurbata muhalli, wanda yace zai taka rawa sosai wajen karkatar da akalar tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.