Isa ga babban shafi
Zaben Zamfara

Kotu ta soke nasarar zaben gwamnan jihar Zamfara

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a birnin Abuja na Najeriya ta soke nasarar zaben Dauda Lawal Dare a matsayin gwamnan jihar Zamfara, inda ta bukaci a sake gudanar da zaben.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare
Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare © The Guardian Nigeria
Talla

 

A ranar 18 ga watan Maris da ya gabata ne Hukumar Zaben Najeriya mai Zaman Kanta INEC ta ayyana Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Sai dai Bello Matawalle na jam'iyyar APC ya kalubalanci sakamakon zaben na Lawaal Dare wanda zya yiz takara karkashin jam'iyyar PDP.

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu a zaben, amma Matawalle wanda a yanzu shi ne Karamin Ministan Tsaro ya ruga kotun daukaka kara don ci gaba da kalubalantar nasararsa.

A wannan Alhamis ne, alkalai uku na kotun suka soke nasarar Lawal Dare, inda suka bukaci a sake gudanar da zaben a wasu kananan hukumomin jihar Zamzfara guda uku.

Kananan hukumomin sun hada da Maradun da Birnin Magaji da kuma Bukuyum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.