Isa ga babban shafi

APC ta roki magoya bayanta da su guji rikici a Kano

Shugaban Jam'iyyar APC a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Alhaji Abdullahi Abbas ya bukaci magoya bayansu a jihar da su guji duk wwani nau'i na tada fitina domin dorewar zaman lafiya.

Nasiru Yusuf Gawuna
Nasiru Yusuf Gawuna © Daily Trust
Talla

 

Shugaban Jam'iyyar ya yi wannan kira ne domin kwantar da hankula jama'a sakamakon zaman dar-dar da ake ciki a jihar bayan yanke hukuncin da ya bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamnan jihar a kotun daukaka kara.

Abdullahi Abbas ya kuma ce hukuncin kotun na yau, ya nuna cewar su ne suka lashe zaben tun farko. 

Kotun daukaka karar ta ki amincewa da bukatar da gwamnatin jam'iyyar NNPP ta shigar ta neman a soke hukuncin kotun kararrakin zabe da ta ce Abba Kabir Yusuf ba shi ne ya ci zaben Kano ba 

Idan za a iya tunawa a wancan karon rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga ta tsawon awanni 24 domin kauce wa barkewar rikici

To sai dai har zuwa wannan lokaci gwamnatin Kanon ba ta ce uffan ba kan hukuncin kotun na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.