Isa ga babban shafi

Ana fuskantar karancin takardun Naira a wasu jihohin Najeriya

A Najeriya ,duk da tabbacin da babban bankin kasar ya bayar a baya-bayan nan na cewa akwai isasshen Naira a kasuwannin kasar , rahotanni sun nuna karancin takardun kudin a fadin Najeriya.

Naira
Naira AP - Sunday Alamba
Talla

Rahotanni daga wasu yankunan kasar na dada nuni cewa an soma fuskantar karancin takardun Nairar a wasu sassan Abuja, Legas, Kano, Kwara, Gombe, Edo, Sokoto, da Ekiti.

 Da yawa daga cikin abokan huldar bankuna da masu sana’ar sayar da kayayyaki, sun koka da yadda ya zama kalubale wajen samun kudi don gudanar da ayyukansu na tattalin arziki.

Tsohon babban Gwamnan bankin Najeriya,Godwin Emefiele da a lokacinsa ya aiwatar da tsarin sabinta kudin Najeriya,ya fuskanci irin wannan matsalla ta karancin takardun kudin Naira,wanda ya kasa magance haka cikin lokaci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.