Isa ga babban shafi

Jam'iyyar NNPP ta bukaci majalisar shari'a ta kasa ta binciki hukuncin kotu

A jihar Kano dake Najeriya Jam'iyyar NNPP  ta bukaci majalisar shari'a ta kasa ta binciki hukuncin da kotu ta dau dangane da batun zaben Gwamnan jihar.Jam’iyyar ta dage cewa, takardar da aka bayar na hukuncin da aka yanke kan karar da ta shigar ya nuna cewa dan takarar gwamnansu ya lashe zaben.

Yadda masu zanga-zanga ke shirin yin tattaki a birnin Kano kenan.
Yadda masu zanga-zanga ke shirin yin tattaki a birnin Kano kenan. © dailytrust
Talla

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ya ce duk da cewa suna kalubalantar lamarin a kotun koli, amma duk da haka suna son majalisar shari'a ta kasa ta fara bincike ba tare da bata lokaci ba.

An shiga rudani a jihar Kano dake arewacin Najeriya, bayan da kotun daukaka kara ta fitar da takardar hukuncin da ta yanke kan shari’ar zaben gwamnan jihar a ranar juma’ar da ta gabata, inda ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.