Isa ga babban shafi

Kotun daukaka kara ta soke zaben 'yan majalisun PDP 11 a jihar Filato

Najeriya – Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke zaben ‘yan majalisun dokokin jihar Filato guda 11 daga jam’iyyar PDP, saboda kin bin umarnin kotu wajen sake zaben shugabannin jam’iyyar kamar yadda aka bata umarni.

Tutar jam'iyyar adawar Najeriya ta PDP
Tutar jam'iyyar adawar Najeriya ta PDP © vanguardngr
Talla

Mai shari’a Okon Abang ya jagoranci alkalai guda 3 wadanda suka yanke hukunci soke zaben ‘yan majalisun guda 11 ba tare da hamayya ba, inda ya bayyana cewar jam’iyyar tayi asarar kuri’un da ta samu gaba daya a zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekara.

Abang yace PDP a jihar Filato ta sabawa sashe na 177 na kundin tsarin mullkin Najeriya na 1999, saboda haka bata da hurumin gabatar da ‘dan takarar da zai shiga zabe.

Nan take kotun ta bai wa hukumar zabe umarni mika takardun nasarar zabe ga daukacin ‘yan takara guda 11 da suka zo na biyu a wadannan mazabun da aka soke zaben su.

Wannan hukunci ya kawo karshen karbe kujerun zaben da jam’iyyar PDP ta samu nasara a jihar Filato, wadanda suka hada da na gwamna da majalisun dattawa da kuma na wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.