Isa ga babban shafi
RIKICIN SIYASA

Tinubu ya sanya mataimakin gwamnan Ondo rubuta takardar murabus

Najeriya – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki wajen samo maslaha a kan rikicin siyasar jihar Ondo, wadda ta farraka gwamna Rotimi Akeredolu mai fama da rashin lafiya da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa, matakin da ya sanya mataimakin rubuta takardar murabus.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

Rahotanni sun ce an dade ba’a ga maciji da juna tsakanin jagororin jihar, abinda ya dada fitowa fili lokacin da gwamnan ya fara jinya a kasar Jamus.

Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Aiyedatiwa
Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Aiyedatiwa © Bayo Onanuga

Yayin jagorantar taron sulhu tsakanin mataimakin gwamnan da ‘yan majalisun jihar, Tinubu ya bukaci dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamnan, yayin da shi kuma aka sanya shi ya rubuta takardar murabus da za’a rike a matsayin kandagarki, domin bashi damar ci gaba da jagorancin jihar har zuwa lokacin da gwamna Akeredolu zai samu lafiya da kuma tababtar da cewar bai yi amfani da mukaminsa wajen cin zarafin magoya bayan gwamnan ba.

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu kuma shugaban gwamnonin kudancin Najeriya
Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu kuma shugaban gwamnonin kudancin Najeriya Twitter/@RotimiAkeredolu

Idan ba’a manta ba, gwamna Akeredolu ya tafi kasar Jamus inda ya kwashe watanni 4 yana jinya, kafin daga bisani ya dawo Najeriya a watan Satumba, amma kuma tun da ya dawo bai taka kafa a jihar Ondo ba, sai ya zauna a Ibadan inda yake murmurewa.

Yayin da yake Jamus, takaddama ta kaure tsakanin magoya bayansa da kuma masu goyan bayan mataimakinsa, a kan wanda ya dace ya ci gaba da tafiyar da ragamar gwamnati.

Kundin tsarin mulki ya baiwa mataimakin gwamna wannan hurumi, amam kuma na kusa da gwamna Akeredolu suka hana shi gudanar da mulkin da kuma aiwatar da manufofin gwamnati, inda suke zargin sa da yunkurin ganin an tsige mai gidansa dake jinya, domin bashi damar zama gwamna.

Wannan ne dalilin da ya haifar da rikici a jihar da kuma bai wa wasu ‘yan majilisu dake goyan bayan gwamnan kaddamar da shirin tsige mataimakin, inda suka baiwa babban jojin jihar umarnin kaddamar da bincike a kansa da zummar kawar da shi.

Jam’iyyar APC ta kasa a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje ta tashi tsaye wajen ganin hakan bai yiwu ba, tare da shirya taron sasanta bangarorin a Abuja, yayin da shi kuma mataimakin gwamnan ya samo umarnin kotu na dakatar da yunkurin.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje © This Day

Bayan sake dawowar matsalar, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyaci ‘yan majalisun jihar da mataimakin gwamnan zuwa Abuja, inda aka gudanar da wannan taro na sulhu wanda ya kunshi baiwa Aiyedatiwa damar ci gaba da jagorancin jihar Ondo a matsayin mataimakin gwamna, da rattaba hannu a takardar murabus din da ba’a sanya mata kwanan wata ba, ko da wata matsala na iya tasowa nan gaba, tare da barin majalisar kwamishinonin jihar kamar yadda take kafin fara wannan rikici.

A nasu bangare, magoya bayan gwamna Akeredolu dake fama da rashin lafiya, zasu bai wa mataimakin hadin kai wajen tafiyar da jihar a kan wannan tsari har zuwa lokacin da gwamnan zai samu lafiya.

Mai magana da yawun majalisar dokokin jihar, Olatunji Oshati ya tabbatar da wannan sulhu da akayi a Abuja a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A watan Oktobar shekara mai zuwa ne wa’adin mulkin Rotimi Akeredolu zai kare, yayin da magoya bayansa ke kokarin ganin mataimakinsa Aiyedatiwa bai samu nasarar zama ‘dan takarar APC da zai maye gurbinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.