Isa ga babban shafi
GARKUWA DA MUTANE

Yankunan Bwari, Kuje da Abaji suka fi hadarin rayuwa a Abuja - FCTA

Najeriya – Lura da yadda matsalar tsaro ke neman zama ruwan dare a sassan Najeriya, hukumomin Abuja sun bayyana yankunan Bwari da Kuje da kuma Abaji a matsayin mafiya hadari wajen rayuwar jama’a saboda yawaitar satar mutane ana garkuwa da su.

Ministan Abuja Nyesome Wike
Ministan Abuja Nyesome Wike © Nyesome Wike
Talla

Ma’aikatar dake kula da Abujan tace duk wasu manyan manya manyan garkuwa da mutanen da aka gani a Abuja sun fito ne daga wadannan yankuna, duk da yake akan samu wasu a wasu yankuna na daban.

Daraktar kula da mulki da kuma kudade na ma’aikatar babban birnin tarayyar, Ebele Molokwu ce ta sanar da haka lokacin da take ganawa da manema labarai domin karin bayani akan ayyukan da sashen ta ya gudanar a wannan shekara.

Molokwu tace yankin Abuja ya yi iyaka da wasu jihohi da matsalar tayi kamari, wanda hakan kan bai wa masu aikata wannan laifi damar kutsa kai Abuja suna satar mutane lokaci zuwa lokaci.

Jami’ar tace suna daukar matakai wajen amfani da dabarun zamani domin tinkarar matsalar wajen ganin sun dakile ta, saboda muhimmancin birnin Abuja da kewaye, da kuma yawan mutanen dake zama a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.