Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin warware matsalar tashin farashin gas

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman don bibiyar yadda farashin iskar gas ta girki ke ci gaba da tashin gwauron zabi a sassan kasar.

Masu sayen iskar gas sun yi layi a Najeriya
Masu sayen iskar gas sun yi layi a Najeriya © the sun
Talla

Wata sanarwar ma’aikatar makamashi ta Najeriyar ta ruwaito minista Ekperikpe Ekpo na bayyana matukar damuwa da yadda farashin na gas ke ci gaba da tashi a sassan kasar.

A cewar ministan cikin kasa da mako guda kwamitin da aka dorawa alhakin warware matsalar zai shawo kan tsadar iskar ta gas da kuma aikin rarraba shi zuwa sassan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, farashin gas din na girki ya tashi daga naira 700 kan duk lita guda da ake saye a baya zuwa fiye da naira 900 a yanzu.

A wasu sassa na Najeriyar bayanai sun ce ana sayar da duk lita guda kan farashin fiye da naira dubu 1da 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.