Isa ga babban shafi

Mutane 30 suka mutu a harin jirgin sojin saman Najeriya kan masu Maulidi a Kaduna

Mutane da dama ne ake fargabar sun rasa ransu sakamakon fashewar wani bam, da ake zargin wani jirgin saman sojojin saman Najeriya ne ya jefa musu, a lokacin da suke gudanar da bukin Mauludi a unguwar Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Jirgin yakin Najeriya
Jirgin yakin Najeriya © Daily Trust
Talla

Duk da cewar babu gamsassun bayanai kan lamarin, amma wasu mazauna garin sun ce mutane 30 sun mutu a hadarin daya faru da cikin daren jiya Lahadi.

“Mutane sun taru suna gudanar da Maulidi sai jirgin sama ya jefa musu bom, wanda yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 30 nan take.”

Sai dai wasu rahotanni na nuna cewar akwai yuwar adadin wadanda suka rasa rayukansu ya zarce 50.

Bayan faruwar lamarin, wasu daga cikin mazauna garin sunyi gudun hijira zuwa makwabtansa, saboda tsoron kar wasu hare-hare su biyo bayansa.

Kawo yanzu dai gwamnatin jahar Kaduna da kuma rundunar sojojin saman Najeriya ba su ce komai kan lamarin ba, duk da dai wasu rahotanni na nuna cewar gwamnatin Jahar ta kira taron tsaro na gaggawa wanda mataimakiyar gwamnan Jahar Dr Hadiza Balarabe ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.