Isa ga babban shafi

A Najeriya an yi kasafin kudin 2024, ba tare da aikin cibiyar samar da wutar Mambilla ba.

Babu wani kasafi da aka ware da ga  kasafin kudin 2024 domin gudanar da ayukan  gina cibiyar samar da wutar lantarki na kimanin Naira biliyan daya a Gembu dake cikin jihar Taraba arewa maso tsakkiyar Najeriyama’aikatar samar da wutar lantarkin kasar za ta kashe Naira miliyan 400 wajen gudanar da taro a kasafin kudin shekarar 2024.

Aikin gina tashar samar da hasken wutar lantarki dake garin Mambila a Najeriya.
Aikin gina tashar samar da hasken wutar lantarki dake garin Mambila a Najeriya. © Twitter / @TarabaFacts
Talla

Aikin samar da wutar lantarkin na Mambilla, wanda ya sha fama da cece-kuce a zamanin tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ana daukarsa a matsayin tashar samar da wutar lantarki mafi girma a kasar, wanda zai iya samar da wutar lantarki mai karfin da ya zarta  Megawatt 3,050 (MW).

Majalisar zartaswar tarayya (FEC) a watan Agustan 2017, ta amince da kasafin kudin dala biliyan 5.792 (kimanin Naira tiriliyan 1.140) don gudanar da aikin.

An ba da kwangilar gina madatsar ce a wani kamfanin kasar China dake aikin samar da  wutar  ta lantarki.

Ministan wutar lantarki na lokacin, Babatunde Fashola, wanda ya tunatar da cewa, Najeriya ta fara magana kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla ne tun cikin shekarar 1972, ya ce an dauki kimanin watanni 72 (shekaru shida).

Tsohon ministan ya ce gwamnatin tarayya tare da bankin kasar  China na Export Import (EXIM). za su  dau nauyin aikin

Ya ce bankin EXIM ne zai bayar da kashi 85 na kudin, yayin da gwamnatin tarayya za ta samar da kashi 15 cikin 100.

Tsarin ayyukan  zai hada da gina madatsun ruwa guda hudu da kuma hanyoyin sadarwa na kilomita 700.

Fashola ya ce, idan aka kammala aikin zai bunkasa tattalin arzikin kasar, domin zai samar da dama ga Mambilla, a fannonin noma,  kiyo, makamashi da kuma yawon  buda ido.a yawon bude ido da

Haka zalika za ta taimaka wa Najeriya wajen dakile matsalar sauyin yanayi da kuma cika alkawarin da ta dauka a karkashin yarjejeniyar Paris, domin wannan zai zama makamashin da ake iya sabuntawa, wanda kuma zai zo kan farashi mai sauki, in ji Fashola.

Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2023, gwamnati ta hannun ma’aikatar wutar lantarki ta ware Naira biliyan 1.1 daga cikin jarin jarin ta na Naira biliyan 232.6 ga aikin.

Wannan ya hada da Naira miliyan 223 na kudin tuntuba, Naira miliyan 100 na masu ba da shawara don tantance al’ummomin da kuma wani kudin tuntuba Naira miliyan 10 na masu binciken filaye.

An kuma ce wani kudin tuntuba na aikin ya lakume Naira miliyan 199; yayin da aka sanya N550m don tallafin takwarorinsu na ayyukan da aka fara.

Binciken da aka yi na kasafin kudin ma’aikatar a shekarar 2024 ya nuna cewa an gabatar da Naira miliyan 400 don taron zuba jari na kasa da kasa da na cikin gida, da taro da baje kolin wutar lantarki; wanda wani sabon aiki ne a cikin kasafin kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.