Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Kotu ta tilasta gwamnatin Kano biyan diyyar rusau

Babbar Kotun Tarraya ta ba da umarnin wucin gadi da ke tilasta Gwamnatin Kano biyan diyyar Naira biliyan 30 ga ’yan kasuwar da ta yi wa rusau a filin idi.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf © Aminiya
Talla

Kotun da ke zamanta a Kano ta bukaci bangaren gwamnatin ya bayyana a gabanta domin ta ji ko suna da dalilin da zai hana aiwatar da umarnin nata.

Mai shari’a I.E. Ekwo na kotun ya ba da umarnin ne kamar yadda takardar hukuncin, dauke da sa hannu magatakardan kotun, Chioma Chijioke, ya nuna, mai dauke da kwanan watan 28 ga Nuwamba, 2023

Sabon umranin kari ne a kan wanda Mai Shari’a S.A Amodeba J ya bayar  a watan Satumba ga kungiyar ’yan kasuwar filin idi da wasu mutane da kamfanoni da suka shigar da karar neman diyya saboda rushe dukiyoyinsu da gwamantin ta yi a watan Yuni.

“Naira biliyan 30 za a biya daga duk kudaden Gwamnatin Kano da ke bankuna da wadanda ta ke samu daga Gwamnatin Tarayya da na sauran asusun ajiyar  wadanda ake kara, kamar yadda Mai Shari’a S.A Amodeba J, ya ba da umarni ranar 29 ga watan Satumba, 2023,” in ji sabuwar hukuncin kotun.

Ta kara da , “umartar wadanda ake kara da su bayyana  a gabanta, ta ji ko suna da dalilin da zai hana aiwatar da umarnin biyar diyyar.

“Masu karar za su ba wa wadanda ake karar takardar hukuncin akalla kwanaki 14 kafin zama na gaba,” in ji Jastis Ekwo.

Sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairu, 2024 domin gwamnatin ta kare kanta.

Hakan na nufin idan gwamnatin ta ki zuwa ko ta kasa kare kanta, to kotun za ta ba da umarnin cirar Naira biliyan 30 din daga asusun ajiyarta da ke bankuna.

Idan abin da ke take da shi a banki bai kai Naira biliyan 30 ba kuma, to za a rufe su, duk kudaden da suka shiga za a cire, har sai an gama cire kudaden.

Yanzu abin jira a ganin shi yadda za ta kaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.