Isa ga babban shafi
TATTALIN ARZIKI

Kamfanin Shell zai zuba sabon jarin dala biliyan 5 domin samar da gas a Najeriya

Najeriya – Katafaren kamfanin hakar man Shell ya sanar da gano wata damar zuba jarin man dake gabar tekun Najeriya da ya kai na dala biliyan 5, yayin da yace zai kashe karin dala biliyan guda tsakanin shekaru 5 zuwa 10 domin inganta aikin da yake yi na samar da makamashin gas domin amfani a cikin gida da kasashen ketare.

Alamar kamfanin man Shell
Alamar kamfanin man Shell REUTERS - ARND WIEGMANN
Talla

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da haka, bayan ganawar da aka yi tsakanin shugaban da daraktan samar da gas na kamfanin Shell, Zoe Yujnovich.

Yujnovic yace kamfaninsu zai zuba wannan sabon jari na dala biliyan 5 ne a gabar ruwan arewacin Bonga dake yankin Neja Delta.

Daraktan yace sun zaku su zuba wannan jari cikin gaggawa, yayin da ya tabbatar da cewar suna son ci gaba da shirin zuba karin jarin da kuma fadada ayyukansu a Najeriya.

Mai magana da yawun kamfanin Shell ya tabbatar da tattaunawar da aka yi tsakanin daraktansu da shugaban Najeriya, amma kuma yaki gabatar da karin haske a kai, saboda abinda ya kira cewar ganawar sirri akayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.