Isa ga babban shafi

Faransa ta bayyana damuwa a kan karuwar cin zarafin mata a Najeriya

Najeriya – Kasar Faransa ta bayyana damuwa a kan karuwar cin zarafin matan da ake samu a Najeriya, ganin yadda alkaluma suka nuna cewar kashi 22 na matan dake kasar sun taba fuskantar wannan matsala.

Jakadaiyar Faransa a Najeriya kenan, Emmanuele Blatmann
Jakadaiyar Faransa a Najeriya kenan, Emmanuele Blatmann © Emmanuele Blatmann
Talla

Jakadiyar kasar Emmanuella Blatmann ce ta bayyana haka wajen wani kwarya kwaryar bikin cika kwanaki 16 na yaki da cin zarafin matan da ya gudana a cibiyar kasar dake Abuja.

Bikin wanda aka saba gabatar da shi kowacce shekara, tsakanin ranakun 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba na baiwa masu fafutukar kare ‘yancin mata damar nazari a kan hanyoyi da suka dace a bi wajen takaita matsalar.

Jakadar Faransa a Najeriya, Emmanuelle Blatmann tare da editan sashen Hausa na RFI, Bashir Ibrahim Idris.
Jakadar Faransa a Najeriya, Emmanuelle Blatmann tare da editan sashen Hausa na RFI, Bashir Ibrahim Idris. © RFI Hausa

Blatmann tace bisa tarihi an fi mayar da hankali a kan yadda maza ke cin zarafin mata saboda yawan matsalar, yayin da ta kara da cewa yanzu a Najeriya ana samun karuwar cin zarafin matan zuwa kashi 22, kuma wasu daga cikin matan mazajensu na aure ne ke musu aika aikan.

Jakadiyar tace lura da yadda matsalar cin zarafin matan ta zama batun kare hakkin bil Adama, ya zama wajibi kowa da kowa ya sanya hannu wajen ganin an dakile aukuwarta.

Blatmann tace hukumar lamini ta duniya IMF, tace irin asarar da ake samu wajen cin zarafin mata a gidaje ko bainar jama’a ko kuma ta kafofin sada zumunta, ya zarce dala triliyan guda da rabi.

Jami’ar ta kuma tabbatar da cewar su kansu maza na muskantar irin wannan matsala ta cin zarafi a gidajensu, amma kuma da yawa daga cikinsu basa iya gabatar da kara a kai domin samun taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.