Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Kamaru sun kaddamar da hari a cikin Najeriya

'Yan tawayen Ambazonia sun tsallako daga yankin kudu maso yammacin Kamaru, inda suka shiga jihar Cross Rivers da ke Najeriya tare da kona gidajen jama'a a garin Belegete da ke Karamar Hukumar Obanliku, sannan suka tsere.

Sojojin Kamaru da ke yaki da 'yan tawayen Ambazonia
Sojojin Kamaru da ke yaki da 'yan tawayen Ambazonia © Panafricanvision
Talla

 

Mayakan na Ambazonia da suka dirar wa garin Belegete a ranar 5 ga watan Disamba, sun kuma sace sama da mutane 40 'yan asalin jihar ta Cross Rivers, yayin da suka kashe wani shugaban yankin, Cif Francis Okweshi.

Rahotanni na cewa, 'yan Ambazonian sun shafe tsawon makwanni biyu suna aika-aika a jihar ta Cross Rivers, lamarin da ya jefa jama'ar yankin cikin fargaba kamar yadda basaraken garin Uchua Amos ya shaida wa manema labarai.

Basaraken ya kara da cewa, har yanzu ba a ji duriyar mutanen da suka rasa muhallansu ba sakamakon firgicin da suka shiga da ya tilasta musu tserewa don tsira da rayukansu bayan sun rasa muhallansu da 'yan tawayen suka kona.

Basaraken ya kara da cewa, ya tuntubi kwamandojin sojojin da 'yan sanda da ke kusa da su, amma jami'an tsaron sun gaza kawo dauki saboda yanayin tudu da kwari na garin.

Ana shafe tsawon sa'o'i shida kafin isa yankin daga wurin shakatawa na dutsen obudu. Motoci ba sa iya ratsawa cikin garin. Don haka yana da matukar wahala ga jami'an tsaronmu su shigo yankin don kawo dauki.

Basaraken ya kuma roki gwamnati da ta jibge jami'anta a garin naa Belegete domin hana 'yan tawayen na Kamaru ci gaba da kaddamar musu da farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.