Isa ga babban shafi

Tikitin jiragen sama a Najeriya sun yi tashin da ba'a taba gani ba

Najeriya – Yayin da jama'a ke shirin fara tafiye tafiye domin halartar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a garuruwansu, rahotanni daga Najeriya sun ce farashin tikitin jiragen sama sun yi tashin da ba'a taba ganin haka.

Kamfanin jiragen sama Aero Contractors na Najeriya
Kamfanin jiragen sama Aero Contractors na Najeriya aero
Talla

Rahotanni sun ce yanzu haka ana sayar da tikitin tafiya guda a kan naira dubu 200 a wasu hanyoyin da jiragen ke zirga zirga.

Wani binciken da Jaridar Daily Trust tayi ya bayyana cewar, duk da tsadar tikitin, tuni masu hannu da shuni suka saye wasu kujerun, domin kaucewa matsala a ranakun da suke shirin suyi tafiyar.

Jaridar tace binciken da ta gudanar ta bibiyan shafukan jiragen saman na nuna cewar, tuni aka sayar da tikiti da dama daga cikin jiragen da aka tsara za suyi zirga zirga a lokacin.

Sakamakon binciken ya nuna cerwar, matsalar tafi kamari a hanyar zuwa Enugu, inda ake sayar da tikiti guda a tsakanin naira dubu 171 zuwa dubu 200, yayin da tikitin zuwa Fatakwal daga Abuja yake tsakanin naira dubu 99 zuwa dubu 138.

Binciken yace tikitin tafiya Sokoto daga Lagos ya kai naira dubu 150, yayin da ake sayar da tikitin Kaduna a kan naira dubu 143, sai kuma Lagos zuwa Ilorin dake tsakanin naira dubu 100 zuwa dubu 143.

Wasu masana na danganta wannan matsalar da tsadar mai da jiragen ke amfani da su, wasu kuma na alakanta matsalar da rashin ingantattun hanyoyin mota, yayin da wasu ke danganta tsadar da matsalar tsaro, lura da yadda 'yan fashi da masu garkuwa da mutane ke yiwa jama'a illa a kan hanyoyin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.