Bankin Duniya ya kaddamar da shirin inganta karatun yara mata a Najeriya
Bankin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya, sun kaddamar da wani sabon shirin hadin gwiwa da ake kira AGILE, da nufin samar da mafita ga rayuwar 'yaya mata da ke matakin manyan azuzun makarantun sakandire.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:05
An samar da wannan shiri ne, domin wayar da kan yara matan matakan da ya kamata su bi wajen kare kan su da kuma ci gaban rayuwarsu.
Haka zalika a cikin shirin, an samar da wani tsarin kwadaitar da iyaye muhimmancin sanya yara mata a makarantu, kama daga dukkanin matakai domin samar da ci gaba a tsakanin al'umma.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Faruk Muhammad Yabo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu