Isa ga babban shafi

Gwamnati ta saukaka wa 'yan Najeriya balaguro saboda Kirismeti

A wani mataki na rage wahalhalun da ake fama da shi na tafiye-tafiyen hutu, gwamnatin Najeriya ta bullo da wasu matakai na kai dauki ga 'yan kasar a lokacin bukukuwa.

Yadda wasu matafiya ke shirin yin balaguro a filin jirgin sama na zzamani da ke birnin Lagos.
Yadda wasu matafiya ke shirin yin balaguro a filin jirgin sama na zzamani da ke birnin Lagos. © Dailytrust
Talla

Sanarwar, wacce gwamnatin kasar ta fitar, ta ce shirin ya hada da zirga-zirgar jiragen kasa kyauta da kuma rage kashi 50% na farashin motocin bas a fadin kasar.

Dele Alake, shi ne ministan ma’adanan kuma shugaban kwamitin ma’aikatun kasa da kasa kan tsoma bakin shugaban kasa, ya jaddada cewa shirin na da nufin baiwa matafiya a cikin gida damar ziyartar ‘yan uwansu da garuruwan su ba tare da damuwa da karin nauyi da tsadar kudin sufuri ba.

An yankewa matafiya a cikin jihohin kasar kudin shiga jirgin kasa, wanda aka tsara zai fara aiki daga ranar 21 ga Disamba zuwa 4 ga Janairu, abin da ya kasance wani Shirin hadin gwiwa ne tare da kamfanonin da ke aiki da manyan motoci a kan hanyoyi 22 a fadin kasar.

Ministan ya kara da cewa, shugaba Bola Tinubu ya amince da wannan shiri, wanda musamman ya fi mayar da hankali ga talakawa, da ke fafutukar yadda za su ciyar da iyalansu.

Ministan Sufuri Sa’idu Alkali ya bayyana aniyar gwamnati na ganin cewa an samu raguwar farashin motocin bas da kuma samar zirga-zirgar matafiya a jirgin kasa kyauta domin sanya walwala a zukatar ‘yan kasar da kuma rage musu radadin tsadar sufuri.

Segun Falade, mai magana da yawun kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasar, ya tabbatar da cewa masu motocin bas za su bi farashin kudin da da aka amince da su, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Wannan kokari na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki na harkokin sufuri na da nufin saukaka wa ‘yan kasa matsalar kudi a lokacin ake samun tangardar nauyin tafiye-tafiye a Najeriya, inda ake samu mafi yawan fasinjojin jiragen sama, da masu bin jiragen kasa a watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.