Isa ga babban shafi
Shari'ar Zaben Kano

Abin da ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar zaben Kano

Kotun Kolin Najeriya ta jinkirta shari'arta game da zaben gwamnan jihar Kano da 'yan kasar suka zaku su gani.

Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna.
Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna. © RFI/HAUSA
Talla

Alkalan kotun biyar karkashin jagorancin mai shari'a Iyang Okoro sun dage shari'ar bayan sun saurari korafe-korafen lauyoyi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Jam'iyyar NNPP su ne daukaka kara zuwa kotun kolin, suna kalubalantar hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar 17 ga watan Nuwamba, wanda ya soke nasarar da gwamnan ya samu a zaben ranar 19 ga watan Maris da ya gabata.

Jam'iyyar ta NNPP ta sanar da Kotun Kolin irin rudanin da aka samu a cikin kwafin takardar shari'ar Kotun Daukaka Karar da ke nuna goyon bayan zaben gwamnan tare da yin umarnin a biya shi naira miliyan 1 saboda bata masa suna.

Alkalan kotun uku karkashian jagorancin mai shari'a Moore A.Adumein, sun goyi bayan karar da Nasiru Gawuna na Jam'iyyar APC ya daukaka.

Kotun ta ce, gwamna Yusuf na NNPP bai yi rajista ba a matsayin mamban jam'iyyar, abin da ya sa ta ce, bai cancanci tsayawa takara ba.

Sai dai a wata doguwar muhawara da aka yi a zauren Kotun Kolin a yau Alhamis, jam'iyyun sun bijiro da wasu batutuwa dangane da matsayin kotun na cewa, gwamna Yusuf ba shi da cancantar tsayawa takara saboda rashin rajistarsa a jam'iyyar.

Kazalika lauyoyin sun hakikance kan cewa, ko Kotun Kolin za ta iya waiwayar abin da hukumar zabe ta INEC ta aikata na rashin rattaba hannu kan takardun kada kuri'a sama da dubu 160 a jihar Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.