Isa ga babban shafi

Kusan jami'an kimiyar gwaje-gwajen likitanci dubu 5 ne suka bar Najeriya a bara

Sama da jami’an da ke kula da dakunan kwaje-gwajen kimiyar likitanci dubu 10 da dari 697 suka bar Najeriya don neman aiki a wasu kasashe.

Sama da jami'an kimiyar gwaje-gwajen likitanci dubu 10 ne suka bar Najeriya don yin aiki a kasashen waje.
Sama da jami'an kimiyar gwaje-gwajen likitanci dubu 10 ne suka bar Najeriya don yin aiki a kasashen waje. AFP
Talla

Magatakardar hukumar Dr Tosan Erhabor ne ya bayyana haka, inda ya ce a yanzu ma’aikatar lafiyar kasar na shirin magance matsalar.

Ya ce da zarar an  fara amfani da tsarin da ake shirin samarwa, zai taimaka wajen sanya ido kan yadda ma’aikatan lafiya ke barin kasar.

“Gwamnati na duba yiwuwar yin bitar mafi karancin albashi da wasu alawus alawus na musamman ga kwararrun jami’am kiwon lafiya. Samar da yanayin aiki mai kyau da inganci na iya zama maganin rage saurin fitar da kwararrun jami’an kimiyar gwaje-gwaje ke yi.”

A cewarsa, sama da masana kimiyyar gwaje-gwaje likitanci dubu 4 da dari 5 da 4 ne suka bar Najeriya a shekarar  2023 da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.