Isa ga babban shafi

Masarautar Kano ta ce dole a daina sata da fataucin kananan yara

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi tir da yawaitar matsalar garkuwa da mutane hade da safarar kananan yara da ake fama da su daga yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayin karbar tawagar kwararrun likitocin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta aike da su zuwa jihar, don yakar annobar coronavirus.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayin karbar tawagar kwararrun likitocin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta aike da su zuwa jihar, don yakar annobar coronavirus. RFI Hausa / Abubakar Dangambo
Talla

Alhaji Aminu Ado Bayero da ya bayyana damuwarsa yayin zantawarsa da manema labarai ranar asabar, ya kuma ce dole a gaggauta magance matsalar.

A ranar 27 ga watan disamban shekarar da ta shude ne rundunar ‘yan sandan jihar Kanon ta sanar da dakile wani baragurbi da ya shahara wajen yin garkuwa tare da safarar kananan yara.

Rundunr ta kuma ce akalla mutane 9 da ke yi wa  baragurbin aiki a jihohin Kano daBauchi, da Lagos, da Delta, da Anambra da kuma Imo suka shiga hannu. Yayin da ta sanar da batun ceto akalla kananan yara 7 akasarinsu ‘yan asalin jihar Bauchi.

Shi ma Shugaban unguwar ‘yan ‘kabilu dake a Kano Boniface Igbekwe, ya yi tir da tsanantar matsalar tare da yin kira hukumomi su yi duk mai yiwuwa wajen kama masu aikata aika aikar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.