Isa ga babban shafi

Kotu ta umarci biyan Emefiele diyyar miliyan 100 kan tsareshi ba bisa ka'ida ba

Babbar kotun Najeriya ta umarci gwamnatin kasar ta biya tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele diyyar tsabar kudi naira miliyan 100 kan tsarewar da aka yi masa ba bisa ka’ida ba.

Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.
Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele. AFP - PHILIP OJISUA
Talla

Shari’ar karkashin jagorancin Alkali Olukayode Adeniyi ya bayyana cewa tsarewar da hukumar tsaron farin kaya ta DSS da hukumar EFCC suka yiwa Mr Emefiele ya sabawa ka’ida da kuma ‘yancin tsohon gwamnan babban bankin.

Tsawon lokaci Emefiele ya dauka tsare a hannun hukumar ta EFCC ta kama shi a ranar 13 ga watan Yuni gabanin umarnin  kotu na sakin shi a ranar 8 ga watan Nuwamba.

Mai shari’ar ya bayyana cewa Emifiele ya gamu da take hakki daga mahukuntan na Najeriya, wanda ya zama wajibi a biya shi diyyar wulakantawar da aka yi masa.

Lauyan da ke kare Emfiele, Mr Mathew Burkaa ya koka gaban kotun kan yadda wanda ya ke karewa ya shafe kwanaki 151 tsare a hannun mahukuntan, lamarin da ya sabawa dokar sa’o’I 48 da aka sahalewa hukumomin tsaro iya tsare mai laifi gabanin mika shi ga kotu.

Tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya na fuskantar tuhumar zargin sace biliyoyin naira lokacin da ya ke rike da mukamin, zargin da Emefiele ke ci gaba da musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.