Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 86 tare da kame 101 a hari kan maboyarsu

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kisan ‘yan ta’adda 86 baya ga kame wasu 101 a hare-haren da suka kai kan maboyar batagari cikin makon da ya gabata a kokarin kakkabe matsalar tsaro a kasar.

Sojin Najeriya yayin shirin afkawa maboyar 'yan ta'adda.
Sojin Najeriya yayin shirin afkawa maboyar 'yan ta'adda. © Nigerian Army - Twitter
Talla

Daraktan yada labarai na rundunar Sojin Najeriyar Manjo Janar Edward Buba yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja jiya Alhamis ya ce dakarunsu basu yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da farmakar ‘yan ta’addan da ke boye dazukan kasar.

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa dakarun sun yi nasarar kame wasu batagari 30 na daban da ke kokarin satar danyen mai baya ga lalata matatun mai da ke aiki ba bisa ka’ida ba akalla 60 a yankin kudu maso gabashin kasar.

Haka zalika a yankin arewa maso yamma Sojin, sun kubutar da wasu fararen hula 21 daga hannun ‘yan garkuwa.

A cewar daraktan yada labaran, kudirin da Sojin suka sa a gaba cikin shekarar nan ta 2024 shi ne tabbatar da sauyi a halin da ake ciki a kasar kana bin da ya shafi matsalolin tsaro.

Rundunar Sojin Najeriya ta bukaci hadin kan al’ummar kasar wajen ankarar da ita game da duk wata maboyar ‘yan ta’adda a lungu da sakon kasar.

Shekaru 14 kenan arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro wanda zuwa yanzu ya sabbaba mutuwar mutane fiye da dubu 40 baya ga tilasta wasu fiye da miliyan 2 barin matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.