Gombe, Bauchi, Borno, na kan gaba wajen matsalar cizon macizai a Najeriya
Ana samun karuwar matsalar harbin macizai da kan rutsa da akalla mutane 500 a cikin kowadanne mutane dubu daya na Nigeria a duk shekara. Jihojin Gombe, Bauchi, Borno, Nassarawa, Taraba, Kebbi, Benue da Oyo ne a kan gaba wajen fuskantar matsalar harbin maciji a kasar. Wakilinmu a Bauchi Ibrahim Malam Goje ya kai ziyara zuwa babban Asibitin Jinyar wadanda maciji ya harba da ke garin Kaltungo a jihar Gombe, ga rahoton da ya aiko mana daga Bauchi.
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:59