Isa ga babban shafi

Sabon gwamnan Ondo ya kori kwamishinonin da suka hana shi rikon kwarya

Najeriya – Sabon gwamnan Jihar Ondo dake Najeriya Lucky Aiyedatiwa ya kori daukacin kwamishinonin da suka hana shi zama mukaddashin gwamna, lokacin da tsohon gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ke fama da rashin lafiya.

Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Aiyedatiwa
Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Aiyedatiwa © Bayo Onanuga
Talla

Wata sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Prince Ebenezer Adeniyan ya rabawa manema labarai, tace Aiyedatiwa ya umarci tsoffin kwamishinonin da su gaggauta mika duk kadarorin gwamnatin dake hannun su ga manyan sakatarorin ma’aikatun su.

Sanarwar ta kuma bayyana sauke duk wasu masu rike da mukaman siyasa da suka kunshi manyan masu bada shawara da kuma mataimakan masu bada shawara nan take.

Daukar wannan mataki na zuwa ne makwanni 3 kacal bayan rasuwar tsohon gwamna Akeredolu da kuma rantsar da Aiyedatuwa a matsayin sabon gwamna.

Takaddama mai zafi ta kaure tsakanin masu goyan bayan tsohon gwamna Rotimi Akeredolu da sabon gwamnan Aiyedatuwa saboda kin amincewarsu ya ja ragamar jihar sakamakon jinyar da tsohon gwamnan ya yi a kasar Jamus.

Kwamishinonin sun hada kai da wasu ‘yan majalisun jihar wajen hana mataimakin gwamnan na wancan lokaci gudanar da aiki, yayin da suka yi kokarin tsige shi daga mukamin sa domin maye gurbinsa da wanda suke so da zummar ganin bai gaji Akeredolu ba.

Lokacin da siyasar jihar tayi zafi, shugaban kasa Bola Tinubu da shugaban APC Abdullahi Ganduje sun kira taron sulhu a Abuja, inda suka sanya Aiyedatuwa sanya hannu a kan takardar murabus kafin bashi damar zaman gwamnan riko.

Makwanni bayan wannan yarjejeniyar da ta gamu da suka daga ciki da wajern jihar, sai gwamna Akeredolu ya rasu, abinda ya sa nan take aka rantsar da Aiyedatuwa a matsayin sabon gwamnan kamar yadda dokar kasa ta tanada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.