Isa ga babban shafi

Najeriya-Hukumar zabe mai zaman kanta ta dakatar zabe a jihohin Akwa Ibom, Enugu da Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da sake gudanar da zabukan da ake yi a wasu mazabu da rumfunan zabe, sakamakon aikin ‘yan ta da zaune tsaye da kuma wasu matsaloli da aka fuskanta.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria
Talla

 

Sam Olumekun, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, shine ya bayyana hakan a ranar Asabar a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan a jihohi 26 da kananan hukumomi 80 a fadin jihohin da abin ya shafa.

Ya bayyana yankunan da abin ya shafa da suka hada da mazabar tarayya ta Ikono/Ini, jihar Akwa Ibom, inda ya ce an dakatar da zabe a rumfunan biyu, EdemUrua 003 a karamar hukumar Ini  da Mbiabong Ikot Udo 003 a karamar hukumar Ikono inda aka kwashe duk kayan zaben.

A jihar Enugu kuma an dakatar da zaben ne a dukkan rumfunan zabe takwas na mazabar jiha ta Enugu ta kudu 1 inda aka rasa ainihin takardar tantance masu zabe kafin a fara aiki.

Hakanan a mazabar Kunchi/Tsanyawa ta jihar Kano a dukkanin rumfunan zaben guda 10 da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon mamayar da ‘yan ta da zaune tsaye suka yi barna.

“Shawarar da hukumar ta yanke ya yi daidai da tanadin sashe na 24 (3) na dokar zabe, 2022. Za a sanar da karin matakan da suka dace ga mazabun da abin ya shafa bayan taron hukumar a ranar Litinin.

“INEC na gayyatar jami’an tsaro da su binciki lamarin, yayin da hukumar ta yi alkawarin yin bincike sosai kan duk wani sabani da ya shafi jami’anta,” in ji Olumekun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.