Isa ga babban shafi
AFCON

Na gamsu da wasannin Zaidu Sanusi - Jose Peseiro

Najeriya – Mai horar da ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya Jose Peserio ya kare Zaidu Sanusi daga sukar da wasu ke masa a karawar da kungiyar ta yi da Angola a ranar juma’ar da ta gabata a gasar AFCON.

Mai horar da 'yan wasan Najeriya José Peseiro
Mai horar da 'yan wasan Najeriya José Peseiro ESTELA SILVA/LUSA
Talla

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana damuwa a kan rawar da Sanusi ke takawa idan Super Eagles ta kai farmaki gidan Angola, amma mai horar da ‘yan wasan kasar Peserio ya kare shi inda yace kokarin da Sanusi ya yi a karawar da Najeriya ta yi da Angola ya ma zarce wanda ya yi a karawar kasar da Kamaru.

Peserio yace a kwallon zamani buga lamba 2 ko 3 na da matukar wahala saboda yadda ake bukatar wadanda ke yin wasa a wadannan bangarori su kai hari da gudu kuma su dawo da gudu, sabanin masu wasan tsakiya dake ‘yan guje guje kadan.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya
Tawagar Super Eagles ta Najeriya © AFCON 2023

Mai horar da ‘yan wasan yace shi ya gamsu da rawar da Sanusi ke takawa a cikin tawagar kungiyar wajen ganin Najeriya ta samu nasara.

Peseiro yace daukacin ‘yan wasan Super Eagles sun yi kokari a karawar ta Angola, kuma sun faranta masa rai tare da sauran ‘yan Najeriya sama da miliyan 200.

Ana saran Najeriya ranar laraba ta kara wasan kusa da na karshe da kungiyar da zata samu nasara tsakanin Cape Verde da Afirka ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.