Isa ga babban shafi

'Yan Sandan Najeriya sun ceto daliban firamaren da aka sace a jihar Ekiti

Najeriya – Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta sanar da ceto wasu daliban firamare guda 5 da malaman su da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Ekiti, abinda ya haifar da mahawar mai zafi a cikin kasar dangane da tabarbarewar tsaro.

Daliban firamaren Ekiti da 'yan sanda suka ceto
Daliban firamaren Ekiti da 'yan sanda suka ceto © Daily Trust
Talla

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta kasa, Olumuyiwa Adejobi yace a jiya asabar jami'an su da taimakon 'yan sandan daji da mafarauta da kuma Amotekun sun kai samamen hadin gwuiwa abinda ya kai ga kubutar da daliban guda 5 da malaman su da kuma direbar motar.

Adejobi yace yanzu haka wadannan dalibai da malaman su na cikin koshin lafiya kuma babu wanda ya samu rauni daga cikin su.

Sace wadannan daliban ta dada haifar da mahawara mai zafi a kan yadda ayyukan masu garkuwa da mutane ke dada fadada a sassan Najeriya, inda wasu ke bada shawarar kafa rundunar 'yan sandan jihohi domin taimakawa jami'an tsaron tarayyar.

A dai dai lokacin da aka sace wadannan dalibai 'yan firamare, a lokacin ne kuma aka hallaka wasu masu rike da sarautar gargajiya guda 2 a yankin.

Rahotan sace wadannan dalibai ta dada zaburar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dake ziyara a Paris, bai wa Sufeto Janar umarnin sake tashi tsaye domin ganin an ceto su da kuma hukunta wadanda ake zargin suna da hannu a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.