Isa ga babban shafi

Shugaban Access Bank Wigwe ya rasu a hatsarin jirgin sama a Calofirnia

Shugaban Access Bank Herbert Wigwe da matarsa da dansa da kuma wasu mutane sun rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a jihar California da ke Amurka, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Shugaban bankin Access
Shugaban bankin Access © kaizenify/wikimedias
Talla

Wigwe  da sauran mutanen sun rasu ne ranar Asabar da safe a agogon Najeriya a yayin da jirginsu yake kan hanyar zuwa birnin Las Vegas.

 

Shugaban Access Bank Herbert Wigwe da matarsa da dansa da kuma wasu mutane sun rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a jihar California da ke Amurka, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

 

Sun rasu ne ranar Asabar da safe a agogon Nijeriya a yayin da jirginsu yake kan hanyar zuwa birnin Las Vegas.

 

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Amurka ta ce ta soma bincike kan musabbabin hatsarin.

 

Ta ce mutum shida ne a cikin jirgin kuma dukkansu ba su tsira ba.

Tsohon shugaban kasuwar hada-hadar hannayen-jari ta Nigerian Exchange Group Abimbola Ogunbanjo na cikin wadanda suka rasu.

 

Tsohuwar Ministar Kuɗi ta Nijeriya kuma shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala ta tabbatar da rasuwar Wigwe da sauran mutanen a sakon da ta wallafa a shafinta na X.

 

“Na yi matuƙar girgiza da samun labarin mutuwar Herbert Wigwe da matarsa da dansa da kuma Bimbo Ogunbanjo a hatsarin jirgin helikwafta,” in ji Okonjo-Iweala

.

 

Ana kallon Wigwe, mai shekara 57, a matsayin daya daga cikin mutanen da suka kawo gagarumin sauyi a tsarin bankunan Najeriya, inda ya taba yin aiki a Guaranty Trust Bank a matsayin darakta kafin ya tafi Access Bank.

Mutuwarsa “babban koma-baya ne” ga fannin bankin Najeriya da na Afirka, a cewar kakakin shugaban Najeriya Bayo Onanuga a sakon da ya wallafa a shafin X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.