Isa ga babban shafi

Najeriya:Tsadar abinci ta jefa mutane da dama cikin halin ha'ula'i

Tashin farashi, musamman na kayayyakin abinci a Najeriya, ya tirsasawa dubban 'yan kasar komawa ga cin wasu nau'oin abincin da jama'a basu saba da su ba. A ci gaba da rahotannin da muke gabatar muku kan tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin kayan abinci, wakilinmu a Bauchi, Ibrahim Malamgoje ya aiko mana da wannan rahotan wanda ya kunshi yadda wata mata ke neman hatsi a shurin tururuwa.

Wani sashi na kasuwar Dawanau da ke Kano a arewacin Najeriya, kasuwar kayayyakin abinci dangin hatsi mafi girma a Afirka.
Wani sashi na kasuwar Dawanau da ke Kano a arewacin Najeriya, kasuwar kayayyakin abinci dangin hatsi mafi girma a Afirka. AP - Sunday Alamba
Talla

‘Yan Najeriya dai su na ta korafi a kan irin halin matsi da suka fada ciki, lamarin da ya sa iyalai da dama ba sa iya cin abinci kamar yadda ya kamata.

Sakamakon tsadar rauwa, al'ummar jihohi da dama a Najeriya suka yi ta gudanar da zanga-zangar neman dauki daga mahukunta.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu  ya janye tallafin man fetur jim kadann bayan rantssar da shi a ranar 29 ga watan Mayun shekarar da ta gabata, lamarin da ya haddasa hauhawar farasin kayayyaki, ya kuma jefa al'ummar kasar cikin halin maatssin rayuwa.

Latsa alamar sauti don sauraron rahoton Ibrahimm Malam Goje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.