Gwamnatin Sokoto ta haramta fitar da kayan abinci zuwa wasu garuruwa
Gwamnatin Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, ta sanar da hana fitar da kayan abinci domin shawo kan tsadar rayuwa da kuma hauhawan farashin da ake fuskanta a jihar. Gwamnatocin jahohi da dama a arewacin Najeriya sun dauki irin wannan mataki, don tabbatar da wadatar kayan abinci a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:34
A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta haramta fitar da kayan abinci zuwa wasu kasashe da ke makwabtaka da ita, inda ko a farkon mako nan sai da aka kama motoci 50 dauke da kayan abinci a jahar Zamfara a kokarin ketawa da su Jamhuriyar Nijar.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Faruk Muhammad Yabo daga Sokoto....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu