Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Kwastam za ta raba wa jama’a kayan abincin da ta kwace

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana shirinta na raba kayan abinci da ta kama ga ’yan kasar domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu.

Wasu ma'aikatan hukumar Kwastam a kusa da shinkafa 'yar waje da ake shigarwa Najeriya.
Wasu ma'aikatan hukumar Kwastam a kusa da shinkafa 'yar waje da ake shigarwa Najeriya. © Daily Trust
Talla

Hukumar ta ce za a yi rabo kayan abincin ne bayan an tantance su an tabbatar da cewa ba su da hadari ga lafiyar dan Adam.

Dubban ’yan Najeriya dai sun gudanar da zanga-zanga a kan tituna kan halin kunci da tsadar kayan masarufi a kasar.

A kan haka ne ranar Talata shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana shirinsu ba raba kayan abincin da aka kama ga ’yan Najeriya.

Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya sanar cewa daukar matakin ya dace da aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na watsa kasa a abinci.

A cewarsa, matakin na gaggawa ne kuma daukar sa na da muhimmanci wajen samun wadatar abinci a Najeriya da kuma dakile illar karancinsa ga ’yan kasa.

“Za a sanar da hanyoyin da za a bi wajen rabon kayan ta ofishin hukumar a duk fadin Najeriya, domin tabbatar da adalci da kuma yin koma a don tabbatar da cewa amfanin ya isa ga wadanda suka fi bukata,” in ji shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.