Isa ga babban shafi

EFCC ta ce ta bankado naira biliyan 60 a cikin kwanaki 100

Hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta sanar da kwato naira biliyan 60 cikin kasa da kwanaki dari, yayin da ta karbi korafe-korafen cin hanci guda dubu biyar.

Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. © EFCC
Talla

Yayin da yake jawabin ayyukan da yayi cikin kwanaki 100 da zaman sa shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce cikin korafe-korafe dubu 5 din da aka shigar gaban hukumar ta amince a fara bincike kan sama da dubu 3 yanzu haka daga ciki.

Ya ce bayan naira biliyan 60 din, an kuma kwato wata dala miliyan 10 cikin kasa da watanni hudu da yayi kan kujerar shugabancin hukumar.

Mista Ola, ya ce lamarin cin hanci da rashawa abu ne da ke bukatar hadin kan jama’ar kasar kasancewar EFCC ba zata  iya gudanar da wannan aiki ita kadai ba.

Shugaban na EFCC ya yi korafi game da karancin ma’aikata a hukumar, yana mai cewa hukumar da ke sanya idanu kan mutane sama da miliyan 150, tana da ma’aikata 4,800 don haka ba za’a ga tasirin aikin da suke yi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.