Isa ga babban shafi

Babu wanda yake da gogewar jan ragamar Hisbah kamar Daurawa - Gadon-Kaya

Akasarin limaman masallatan Juma’a a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a hudubarsu ta tabo batun sauka daga shugabancin hukumar Hisbah da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi.

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Dakta Abdallah Gadon-Kaya kenan.
Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Dakta Abdallah Gadon-Kaya kenan. © GadonKaya
Talla

Fitaccen malamin nan, Dakta Abdallah Gadon-Kaya, ya bayyana cewa abin takaici ne a rasa Malami irin Daurawa, wajen yaki da ayyukan badala a jihar da ta kasance ta yi kaurin suna sosai a yankunan Hausawa da ke bisa tafarkin musulunci.

“Duk masoya manzon Allah (S.A.W) basu ji dadin wannan mataki na Mallam ba, amma ina da yakinin cewa masu son yada badala yanzu haka suna nan suna ta tafi suna murna, bukatarsu ko kuma hakarsu ta cimma ruwa amma a ganin su,” in ji Gadon Kaya.

Malamin wanda ya bayyana hakan a hudubar juma’ar da ya gabatar yau a garin Kaduna, Ya ce jihar Kano, tayi kaurin suna wajen bawa addinin musulunci gudun mowa sosai a duniya.

Dakta Gadon-Kaya ya jaddada cewa Sheikh Daurawa, Malami ne da bai kamata gwamnati ta yi asarar sa ba, musamman idan aka yi la’akari da irin gudun mowar da ya bayar a hukumar Hisbah, ciki kuwa har da shawarwarin da ya kawo da suka kunshi auren zawarawa, taimakawa marayu da kuma yadda za a gyara halayyar yaran da suke kokarin fusata al’umma.

“Bana jin a iya sani na akwai wani Malami da ya samu gogewa wajen tafiyar da harkar Hisbah, kamar Sheikh Aminu Daurawa,” a cewar Malamin.

Dakta Gadon-Kaya ya ce da alama maganganun da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kan yadda Hisbah ke gudanar da ayyukanta, yana daga cikin abin da ya sa shugaban hukumar ajiye mukaminsa.

Malamin ya kuma shawarci gwamnan na Kano, da ya zauna tare da Sheikh Daurawa domin bashi hakuri da kuma shawarwari, domin barin shugabancin hukumar da ya yi ba karamin gibi bane ga jihar Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.