Isa ga babban shafi

Lokaci ya yi da mace za ta jagoranci Najeriya saboda maza sun gaza - PDP

Babbar Jam'iyyar adawa ta Najeriya PDP ta bayyana cewa maza sun gaza, a don haka lokaci ya yi da ya kamata a bai wa mace damar jagorantar kasar, yayin da jam'iyyar ta koka kan halin da kasar ta tsunduma a ciki.

Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban Najeriya daga jam'iyyar APC
Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban Najeriya daga jam'iyyar APC © AP - Ben Curtis
Talla

Mukaddashin shugaban Jam'iyyar PDPd, Ambasada Umar Damagum ne ya bayyana haka a yayin gabatar da jawabi a taron da Ofishin Shugabar Matan Jam'iyyar ya shirya albarkacin zagayowar Ranar Mata ta Duniya a yau Juma'a, yana mai cewa, tun fil azal  matan sun yi fice wajen sasanta rikice-rikice.

Mukaddashin shugaban na PDP wanda sakataren jam'iyyar Sanata Samuel Anyanwu ya wakilce shi, ya bayyana cewa, ba za a iya kayyade muhimmancin iyaye mata da matan ba, yana mai fatan wata rana mace za ta zama shugabar Najeriya lura da yadda mazan suka gaza jagoranci.

 

“That is why the founding fathers of PDP know the role of women and that is why today in Nigeria, no matter how you look at it , PDP is the most democratic party in Nigeria and Africa. This is the only party that gives opportunity to women to aspire to any position free of charge without buying any form. We do that because we want to encourage women.

Wannan ne dalilin da ya sa mutanen da suka assasa jam'iyyar PDP suka fahimci muhimmancin mata , abin da ya sa aka wayi gari jam'iyyar ta zama mafi riko da tsarin dimokuradiyya a Najeriya da Afrika. Wannan ce jam'iyyar da ke bai wa mata damar neman ko wacce irin kujera kyauta ba tare da sayen fom ba. Mun yi haka saboda muna son mu karfafa musu guiwa. Inji Damagun. 

A yayin gabatar da jawabin maraba da baki, Shugabar Matan Jam'iyyar PDP, Hon. Amina Divine Arong ta ce, dimokuradiyya za ta armashi ne muddin aka zabi karin mata a mukamai na siyasa.

 

Abin bakin ciki ne yadda aka bar mata a baya duk kuwa da irin rawar da suke takawa wajen samar da sauyi a fagen siyasa. Inji Arong.

Yau ce dai ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazari kan al'amurran da suka shafi mata domin samar musu da ci gaba a rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.