Isa ga babban shafi

Hisba a Kano ta cafke mutanen da ke cin abinci da tsakar rana a Ramadan

Jami’an hukumar Hisba a jihar Kano ta arewacin Najeriya sun sanar da kame wasu mutane 11 sakamakon samunsu da laifin cin abinci da tsakar dai dai lokacin da al’umma ke azumin watan Ramadana.

Shugaban hukumar Hisba a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Shugaban hukumar Hisba a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. © AfricaTV3
Talla

Kakakin hukumar ta Hisba Lawal Fagge ya ce mutanen 11 sun kunshi maza 10 da kuma wata mace guda da aka samu ta na tallar gyada ta kuma tafe tana ciye-ciye.

A cewar kakakin na Hisba mutanen 10 dukkaninsu an kama su ne gab da kasuwa kuma babban laifin shi ne yadda suke ciye-ciye cikin jama’a da rana tsaka duk da masaniyar kasancewar kowa bakinsa a rufe.

Tuni dai mutanen 11 suka amsa laifinsu wadanda aka damka su ga iyalansa bayan alkwarta yin azumin watan na Ramadana.

Duk da kasancewar azumin watan na Ramadana bai shafi wadanda ba musulmi ba, amma hukumar ta Hisba ta ce su kansu za su iya fuskantar hukunci matukar aka same su da laifin sayar da abinci ga musulmi da rana tsaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.