Isa ga babban shafi
EID EL FITR

Dalilin da ya sa muka gudanar da sallar Eid el Fitr a yau - Sheikh Lukuwa

Najeriya – Wasu al'ummar Musulmi a Jihar Sokoto dake Najeriya, a karkashin jagoranci Sheikh Ayuba Musa Lukuwa, sun gudanar da Sallar Eid el Fitr, sabanin sauran jama'ar kasar, yayin da suka gabatar da hujjojin da ya sa su aje azumin su.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar © Daily Trust
Talla

Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da cewar sakamakon rashin ganin jinjirin watan shawwal jiya litinin, al'ummar Musulmin Najeriya za su bi sahun na Saudi Arabia da wasu kasashen Larabawa domin gudanar da bikin sallar gobe Laraba.

Sai dai Sheikh Lukwa yace sakamakon ganin jinjirin wata a Jamhuriyar Nijar wadda ke makotaka da Najeriya ya zama wajibi su aje azumin da suka yi da kuma gudanar da sallar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Lukwa yace sun samu tabbacin ganin watan na Nijar a sakonnin bidiyo da aka yada, wada ya bayyana yau a matsayin ranar sallar idi, saboda haka babu dalilin da za su ci gaba da azumi.

Shehun malamin yace indai har zasu karbi sanarwar Saudi Arabia, babu dalilin da za su ki karbar na Jamhuriyar Nijar dake makota da su.

Malamin yace ba yace dole ne kowanne Musulmi ya yi sallah yau ba, amma kuma babu wata hujja da su zasu ki yi bayan an ga watan a Nijar dake kusa da su.

Shehun malamin ya dade yana zargin Sarkin Musulmi Abubakar da tilastawa jama'a karbar ganin watan Saudiya wanda yace ya sabawa koyarwar Manzon Allah, Annabi Muhammad, SAW.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.