Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kano zata gurfanar da Ganduje da uwargidansa a kotu ranar 17 ga watan Afrilu

Najeriya – Wata Babbar kotu a Kano dake Najeriya ta sanya ranar 17 ga watan nan a matsayin ranar da za'a gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da uwargidansa da kuma wasu mutane 6 domin tuhumar su da laifin cin hanci da rashawa.

Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da wanda ya gaje shi Abba Kabir Yusuf
Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da wanda ya gaje shi Abba Kabir Yusuf © DailyTrsut
Talla

Jaridar Daily Trust tace za'a gabatar da tuhume tuhume guda 8 ne a kan tsohon gwamnan da suka hada da cin hanci na dalar Amurka dubu 413 da karkata naira biliyan guda da miliyan 380 kudin talakawa.

Jaridar tace takardar karar ta kunshi sunayen Abdullahi Umar Ganduje da Hafsat Umar da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad da Kamfanin Lamash da masakar Safari da kuma Lesage.

Gwamnatin Kano da ta gabatar da karar tace ta shirya shaidu guda 15 da za ta gabatar a kotun,yayin gudanar da wannan shari'ar, yayin da alkali Usman Na'abba na babbar kotun jihar ta 4 ya sanya ranar 17 ga wata a matsayin ranar fara sauraron karar.

Babban lauyan gwamnatin jihar Haruna Isah Dederi ya tabbatar da shigar da karar, kuma kotu zata zauna a kai, amma bashi da tabbacin ko an iya gabatar da takardun tuhumar ga wadanda ake zargi.

Dederi ya kara da cewar abinda tsohon gwamnan bai sani ba shine babu yadda za'a yi ya tserewa shari'a, kuma matakin zai zama darasi ga masu rike da mukaman gwamnati.

Babban lauyan yace ikrarin Ganduje cewar ba za su iya gurfanar da shi a gaban kotu ba, ya saba ka'ida domin laifuffuka ne da suka shafi na bangaren jiha, wanda ba shi da hurumin tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.