Isa ga babban shafi
'YAN BINDIGA

Muna samun nasarar yaki da 'yan bindiga a Najeriya - Ribadu

Najeriya – Gwamnatin Najeriya na samun gagarumar nasara wajen tabbatar da tsaro a sassan Najeriya, amma kuma ta gwammace ta ci gaba da aiki maimakon yayata nasarorin da take samu a bainar jama'a.

Malam Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro
Malam Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro © RFI Hausa
Talla

Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.

Ribadu yace gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, da zaran ta samu labari, kuma wannan na daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu tun daga watan Yunin da ya gabata.

Mai bada shawarar ya tabbatar da matsalolin tsaron da suka addabi kasar da kuma irin illar da suka yiwa jama'a, yayin da yace suna aiki tare da gwamnonin jihohi domin ganin an shawo kan ta da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust

Ribadu ya bayyana cewar yawan magana kan yi illa ga nasarorin da ake samu, abinda ya sa suka gwammace su ci gaba da aiki ba tare da shelar abinda suke yi ba.

Mai bai wa shugaban shawara yace duk wadanda aka kama da sunan garkuwa da mutane a yankin arewacin Najeriya da gwamnati ta samu labari ya zuwa wannan lokaci ta kubutar da su, kuma gwamnati zata ci gaba da wannan aikin ba tare da kaukautawa ba.

Yace daga cikin wadanda aka kubutar harda dalibai da mazauna kauyukan da aka yi garkuwa da su, domin gwamnati tayi nasarar ganin sun samu yancin kan su.

Ribadu ya kuma jaddada cewar basa biyan kudin fansa wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, sabanin zargin da wasu jama'a keyi, yayin da ya bayyana cewar an samu nasarori da dama a jihohin Sokoto da Zamfara da Kaduna da kuma Neja.

Sheikh Gumi a yayin ziyarar wasu 'yan bindiga a jihar Kaduna
Sheikh Gumi a yayin ziyarar wasu 'yan bindiga a jihar Kaduna © dailytrust

Mai bai wa shugaban shawara yace tun da wannan gwamnati ta hau karagar mulki ba'a taba nasarar kai hari gidan yari ko mujami'a ko barikin soja ba kamar yadda aka saba yi a hsekarun baya, yayin da yanzu ko cikin dare kana iya tafiya Kaduna da Kano daga Abuja.

Ribadu ya nemi taimakon Ubangiji wajen samun nasarar wannan matsala baki daya a Najeriya, musamman a yankin arewacin kasar, yayin da yace masu aikata wadannan laifuffukan 'yan uwa ne kuma daga addini guda, inda ya danganta lamarin da masifa.

Mai bada shawarar yace shugabannin yanzu na aiki a kai tukuru domin tinkarar matsalar kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.