Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun mika makamansu ga gwamnatin jihar Filato - Gwamnati

Gwamnatin jihar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ‘yan ta’addan da ke addabar yankin karamar hukumar Wase, sun mika mata bindigunsu kirar AK47 da dama.

Gwamnatin jihar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ‘yan ta’adda sun mika mata bindigunsu kirar AK47 da dama.
Gwamnatin jihar Filato da ke Arewacin Najeriya ta ce ‘yan ta’adda sun mika mata bindigunsu kirar AK47 da dama. © Daily Trust
Talla

Mai taimaka wa gwamna Caleb Mutfwang na jihar bangaren tsaro da kuma shugaban rundunar Operation Rainbow Birgediya Janar Gakji Shippi ne, su ka bayyana haka a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Jos babban birnin jihar.

Janar Shippi ya bayyana cewar mika makaman da ‘yan bindigar suka yi, ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakaninsu da gwamnatin jihar.

Ya ce bayaga bindigu kirar AK47, akwai wasu nau’ikan makamai da ‘yan bindigar suka mika wa gwamnati, matakin da ya ce ya nuna irin kokarin da gwamnati ke yi wajen raba al’umma da makamai.

Kwamandan rundunar ta Operation Rainbow, ya ce ana ci gaba da kokarin ganin wasu karin ‘yan bindigar sun mika makamansu ga gwamnati, don rage yawaitar kai hare-hare a yankin karamar hukumar Wase.

Jihar Filato dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro da rikicin addini a Najeriya, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma ta dukiya mai tarin yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.