Isa ga babban shafi
Cutar Ƙyanda

Cutar ƙyanda ta kashe aƙalla yara 42 a arewa maso gabashin Najeriya

A Najeriya, yara ƙanana 42 ne suka mutu sakamakon harbuwa da cutar ƙyanda a cikin mako guda a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana a jiya Juam’a.

Wata yarinya da ke fama da cutar ƙyanda.
Wata yarinya da ke fama da cutar ƙyanda. REUTERS - HEREWARD HOLLAND
Talla

Kwamishinan lafiya na jihar ta Adamawa, Felix Tangwami ya ce cutar ƙyandar ta shafi ƙananan hukumomi biyu ne, inda aka samu rahoton mutuwar yara 42 daga cikin 200 da suka harbu da cutar.

A wani taron manema labarai, kwamishinan ya ce ma’aikatarsa ta aike da jami’ai da allurar rigakafi zuwa yankunan da abin ya shafa.

Ƙyanda, ƙwayar cuta ce mai saurin yaduwa, kuma tana kama yara ne da ke ƙasa da shekaru 5 da haihuwa. Ana iya samun kariya daga cutar ta wajen karɓar allurar rigakafi.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce sama da mace-mace masu nasaba da cutar ƙyanda har miliyan 50 ne aka kauce wa sakamakon allurar rigakafi tun daga shekarar 2000.

Ta’azzarar matsalar tsaro a yawancin jihohin arewacin Najeriya ne aka ɗora laifi katse shirin rigkafi a yankin, lamarin da ya jefa yara kanana a yanayi na rauni.

Bullar annobar Covid -19 na daga cikin matsalolin  da suka kawo naƙasu ga tsarin kiwon lafiya a sassan ƙasar, kamar yadda wani rahoton ƙungiyar likitoci na duniya MSF ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.